Simi Mawakiyar Hip Hop Ta Kushe ‘Yan Nigeria

100

- Advertisement -

Shahararran mawakiyar Nijeriya, Simisola Bolatito Ogunley wacce aka fi sani da suna Simi, a wani fira da kafafa mujallar The Sun ta yi da ita na musamman ta yi bayyani akan sabuwar kudin wakar ta, tare da rayuwar soyayyar ta, da wadan su jawabi akan da maza.

A lokacin da aka tambaye ta ko mazan Nijeriya sun iya soyayya?, tauraruwa ta bayyana cewa A’a.

Inda ta bayyana cewa mazan Nijeriya na ganin cewa ba sai sun iya soyayya ba. Ba wai nayi wannan maganan bane don na tsokane wani bane, ta ce.

bu wanda ya isa ya sa mazan Nijeriya su yi abunda ba su ga dama ba, sabili da haka suna ganin suna da damar yin duk abunda suka ga daman yi. Sun yadda da cewa suna da damar yin komai. Ranan nan, ina kallon wani fim din Nijeriya na Nollywood.

Akwai wani mutum da ya bar matarsa saboda zai je ya hadu da wata budurwarsa a waje. Mutumin na ta kwana da matan awaje yadda yake so.

Ina jin ya yiwa wannan budurwan na sa ciki a fim din, bayan faruwan haka sai suka zo suka fada da ita wannan budurwan na sa wadda ya ma ciki, har ya sa suka rabu.

Sai ya koma gidan iyayen matarsa zai dawo da matan shi, mahaifiyar matan na shi ta sa ‘yar ta ta durkusa a gaban mijin na ta, ta ba shi hakuri.

Abunda ya dade yana damu na, ya mani zafi sosai. Gaskiyan al-amarin shine hakan abun yake. Mazaje da dama a wannan kasar sun girma suna ganin suna da damar yin duk abunda suka dama yi.”

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.