Mourinho Ya ce Pogba Ya Ji Rauni A Ranar Juma’a

33

- Advertisement -

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Paul Pogba yaji rauni a lokacin da yan wasan kungiyar suke daukar horo a ranar Juma’a wanda hakan yasa bai buga wasan da kungiyar ta lallasa Liverpool ba da ci 2-1.

Mourinho yace dan wasan yaji rauni kuma likitocin kungiyar sun bayyana cewa bazai iya buga wasan da kuniyar ta buga da Liverpool ba saboda haka yana jiran rahoto akan ciwon nasa a gobe Litinin.

Ya cigaba da cewa Pogba bashi da sa’a wajen jin ciwo kuma kamar Pogba, shima baiji dadin ciwon da dan wasan yatafi ba saboda haka yana bakin ciki da faruwar wannan lamari mara dadi.

Sai dai an tambayi Mourinho cewa ko Pogba zai iya buga wasan da kungiyar zata buga da Sebilla a gasar zakarun turai? Sai Mourinho yace shima bai sani ba saboda haka yana jiran bahasi daga wajen likitocin kungiyar.

Manchester United dai ta lallasa Liverpool daci 2-1 a filin wasa na Old Trafford ta hannun dan wasa Marcos Rashford wanda duk shine ya zura kwallayen guda biyu a dai-dai minti na 14 da 24 da fara wasa sai dai dan wasan baya na kungiyar, Eric Bailly yaci gida bayan andawo daga hutun rabin lokaci.

A ranar Talata ne Manchester United zata karbi bakuncin Sebilla wadda zata zo daga kasar sipaniya a wasa na biyu na gasar zakarun turai bayan da aka buga 0-0 a wasan farko da suka buga a kasar sipaniya.

Please Share.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.