Anyiwa Wakilan Kwankwaso Korar Kare

23

- Advertisement -

Rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewar jami’an tsaro sun kori wakilan tsohon gwamnan Kano kuma Sanatan Kano Ta Tsakiya wato Dr. Rabiu Musa Kwankwaso daga wajen daurin auren ‘yar hamshakin dan kasuwa Fatima Aliko Dangote.

Majiyar ta tabbatar da cewa bayan shigar su wajen aka rika fito da su daya bayan ana umartar su da su bar wurin daurin auren.

‘Yan sanda sun kori wakilan Kwankwaso a wurin auren diyar Dangote

Babu wani takamaiman dalilin da jami’an ‘yan sandan su ka bayar na korar wakilan na Kwankwaso.

Wasu ma su fashin baki a kan al’amuran dake faruwa a jihar Kano, musamman tsakanin tsohon gwamna Kwankwaso da gwamna mai ci, Ganduje, na alakanta korar wakilan Kwankwaso da kalamansa a kan daurin auren diyar gwamna Ganduje da dan gwamna Ajimobi.

Kwankwaso ya soki auren diyar Ganduje da cewar auren zawarawa ne, kalaman da ba su yiwa bangaren magoya bayan gwamna Ganduje.

Ma su nazarin siyasar Kano na ganin cewar abu ne mai matukar wuya a iya yin sulhu tsakanin tsohon gwamna Kwankwaso da gwamna Ganduje, tsohon mataimaki ga Kwankwaso.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.