Kwankwaso, Obasanjo, tsofin gwamnoni, da jam’iyyu 35 na cigaba da kulle-kullen siyasa

32

- Advertisement -

– Tsohon shugaban kasa Obasanjo, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, da wasu manyan-manyan ‘yan siyasa daga fadin kasar nan na cigaba da ganawan domin shirya tunkarar 2019

– A daya daga cikin irin wannan ganawa da ta gudana a Protea Hotel dake jihar Legas, Obasanjo, ya gana da shugabancin wasu jam’iyyu 35

– Wata majiya daga cikin wadanda su ka halarci taron ta bayyana cewar Obasanjo na son a hada karfi da karfe domin karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas, Donald Duke, da wasu manyan-manyan ‘yan siyasa daga fadin kasar nan na cigaba da ganawa domin shirya tunkarar 2019 dake kara karatowa.

A daya daga cikin irin wannan ganawa da ta gudana a Protea Hotel dake jihar Legas, Obasanjo, ya gana da shugabancin wasu jam’iyyu 35 karkashin kungiyar Hadaka ta jam’iyyun Najeriya. Daga cikin jam’iyyun das u ka halarci taron akwai; Social Democratic Party (SDP), Labour Party (LP), Alliance for Democracy (AD), Democratic People’s Congress (DPC), Action Alliance (AA), Progressives People’s Alliance (PPA), Democratic Alternative (DA) and National Conscience Party (NCP).

Kwankwaso da Obasanjo

Obasanjo dai na son hada kan wasu ‘yan siyasa da jam’iyyun Najeriya domin bullo da hanyoyin da za’a bi domin karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.

Daga cikin manyan ‘yan siyasar da su ka halarci taron sun hada da; Mr. Olisa Agbakoba (SAN), dan tsohon firaministan Najeriya Tafawa Balewa; Dakta Jhalil Tafawa-Balewa, wakilin jam’iyyar AAP; Mista Kenneth Udete, da Mista Okey Chukwuendu, wanda ya wakilci jam’iyyar AGAP.

Wata majiya daga wadanda su ka halarci ta sanar da cewar Obasanjo ya shaida ma su cewar hada karfi da karfe ne kadai zai ba su dammar karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.