Download Video:- Da Ganduje Yake Karyata Cewa Ya Karbi Cin Hanci

2,569

- Advertisement -

Majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kaddamar da kwamiti na mutum bakwai domin yin bincike a kan wasu jerin bidiyo da ke ikirarin nuna gwamnan jihar da karbar “cin hanci” daga wajen wasu ‘yan kwangila.

A makon da ya gabata ne jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labaranta a intanet ta saki labarin da ke cewa wani gwamna a yankin arewa maso yammacin kasar wanda ke neman zarcewa a mulki karo na biyu, yana karbar makudan kudade a wajen wasu ‘yan kwangila.

A ranar Lahadi ne kuma mawallafin jaridar Ja’afar Ja’afar ya saki bidiyo na farko daga cikin kusan 15 da ya ce yana da su, a shafin jaridar tasa.

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta musanta wannan zargi.

Wani dan majalisar dokoki da ke wakiltar karamar hukumar Warawa Alhaji Labaran Abdul Madari ne ya gabatar da bukatar a yi bincike kan lamarin duba da muhimmancinsa, inda kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar birni da kewaye Alhaji Baffa Dan Agundi ya goyi bayan hakan.

Ga Video Nan Kasa:-

👇👇👇👇👇

Download Video Now
Kara ta cikaken Bayani:- Ganduje Ya Karbi Cin Hanci Ga ‘Yan Kwangila

Source @ Dailynigeria.com

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.