Duniya Tazo Karshe, Babban Malamin Addini Yayima Mata 20 Ciki lokacin Karantar Da Su

100

- Advertisement -


Jami’an yan sanda reshen jihar Enugu sun kama wani fasto bisa laifin yi ma mambobin cocinsa su 20 ciki.
Faston mai shekara 53 mai suna Timothy Ngwu ya kasance babban mai kula da cocin Vineyard Ministry of the Holy Trinity dake Enugu.

An rahoto cewa yayi ikirarin cewa ruhu mai tsarki ya bashi umurni da yayi ma mambobin cocinsa mata ciki.

Kakakin rundunar yan sandan Enugu, Ebere Amaraizu ya bayyana cewa an gurfanar da faston bisa laifin keta hakki.

Majiya kusa da cocin faston sun bayyana cewa faston yana ikirarin cewa yana biyayya ne ga umurnin ruhu da ya aikata abunda Allah yayi umurni, ba tare da yin la’akari da ko suna da aure ko basu da aure ba.

Majiyinmu ya cigaba da bayyana cewa a duk lokacin da wadanda yayi ma cikin suka haifi yara, ana barin yaran da iyayensu mata a cocin har karshen rayuwarsu.

An tattaro cewa an matarsa ce ta kai karar faston ga yan sanda bayan ta gaji da mugun aikin da yake tafkawa bayan ya yiwa yar uwarta ciki duk cikin umurnin ‘biyayya ga Ubangiji’.

Yayin da yake kare kansa, faston ya bayyana cewa, har ila yau, bai taba saduwa da kowanne daga cikin matan ba face da amincewa akan bukatan ruhu.

Haka zalika, an dauko daga bakin shi yana fadin cewa yana da mata biyar da yara 13 tare da kwarkwara da dama wadanda ya samu bayan umurnin da ‘ruhu ya bashi’.

Source www.PressHausa.com

- Advertisement -

1 Comment
  1. […] Ku Shiga Nan:- Domin Cigaba Da Karantawa, Yadda Anka Yanke mai Hukunci […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.