Download Video:- Yadda aka tilastawa daliba cire hijabi kafin ta shiga makaranta a Ibadan 

132

- Advertisement -

Wani bawan Allah ya yi korafin yadda masu tsaron makaranta a garin Ibadan suka tilastawa diyarsa cire hijabinta kafin ta shiga makarantar.

Kamar yadda aka haska a faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, mai tsaron makarantar ya umurci wasu dalibai mata su cire hijibinsu kafin su shiga makarantar.

Mai tsaron makarantar ya ce “Ku cire hijabin, idan kun fito daga harabar makaranta sai su saka. Idan kun fita waje babu wanda ke da ikon hana ku saka hijabi.”

Download Nigerian Top Blogs App here
Wasu mutane da ke tsaye a wurin da abinda ya faru sun goyi bayan mai tsaron makarantar yayin da wata mace ta masa gargadin cewa yana neman rikici ne.

Daga bisani mahaifin dalibar ya zo kofar makarantar da kansa amma masu tsaron makaranta suka fada masa cewa an basu umurni daga sama ne cewa kada su kyalle dalibai su rika shiga makaranta sanye da hijabi.

Mahaifin daliban ya yi ikirarin cewa mai tsaron makarantar ya samu daurin gindi ne daga wasu ma’aikatan jami’ar Ibadan.

Mahaifin daliban ya koka kan cewa ba dai-dai bane a hana diyarsa shiga makaranta da hijabi duba da cewa ya biya mata kudin makaranta.

Download Video Now

 Source www.PressHausa.com

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.