Bayan fitowar sunayen ministocin Buhari: ‘Yan Kannywood na kiran a baiwa Ali Nuhu ministan wasanni

99

- Advertisement -

Tun kamin fito da sunayen sabbin ministocin shugaban kasa, Muhammadu Buhari labarai ke yawo cewa za’a baiwa tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Ministan wasanni, bayan fitowar sunayen a Jiya, Talata, wasu taurarin Kannywood sun fara kiran cewa ya kamata a baiwa Alin mukamin minista.

Ali Artwork na daya daga cikin wanda suka fara wannan kura inda ya rubuta a shafinshi na Instagram cewa, ko suna so ko basa so muna nan akan bakanmu na cewa sai an baiwa Ali Nuhu ministan wasanni.

Hakanan shima Abbas Sadiq yayi kiran cewa ya kamata a baiwa Ali Nuhun ministan wasanni dan ya cancanta.

Taurarin masana’antar Kannywood sun bayar da gudummuwa sosai kisan za’a iya cewa fiye da ta kowane lokaci a baya a babban zaben 2019 wanda shugaba Buhari ya samu nasara.

Source www.PressHausa.com

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.