Lukaku Zai Taimakawa Inter Milan Sosai, Cewar Eto’o

35

- Advertisement -

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan da Barcelona, Samuel Eto’o, ya tabbatar da cewa sabon dan wasan Inter Milan, Rumelu Lukaku, wanda ya koma kungiyar daga Manchester United zai taimakawa sabuwar kungiyar tasa da yawan cin kwallayen da yake yi.

Lukaku dai yakawo karshen zaman shekara biyu da yayi a Manchester United bayan daya koma domin cigaba da buga kwallo da kociyan Inter Milan, Antonio Conte, wanda yake son dan wasan tun yana tsohuwar kungiyarsa ta Everton.

Tun bayan da kociyan Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya karbi aikin koyar da kungiyar aka fara dan ganta Lukaku da barin kungiyar sbaoda ya bayyana cewa dan wasa Marcus Rashford shine zai zama dan wasansa na gaba.

Sai dai Samuel Eto’o, wanda yana cikin ‘yan wasan da suka lashe kofi uku a Inter Milan a shekara ta 2010 a lokacin Jose Mourinho ya bayyana cewa hankalin Lukaku ya kwanta kuma zai bawa duniya mamaki.

“Ina yi maka barka da zuwa Inter Milan Lukaku kuma ka samu damar zuwa babbar kungiya wadda take cike da manyan ‘yan wasa saboda haka zaka cigaba da zura kwallaye a raga kamar yadda ka saba a kowacce kungiya” in ji Eto’o

Lukaku dai ya zura kwallaye 12 a kakar wasan data gabata a Manchester United a wasannin firimiyar daya bugawa kungiyar sannan kuma gaba daya ya zura kwallaye 42 cikin wasanni 96 daya bugawa kungiyar tun bayan daya koma daga Eberton akan kudi fam miliyan 74.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.