Shugaban hukumar zaben River ya tsaya takarar gwamna

38

- Advertisement -

Batun aniyar tsayawar shugaban hukumar zaben jihar Cross Rivers, Dr Frankland Briyai dan takarar neman gwamnan jihar Bayelsa da ke tafe a ranar 16 ga Nuwamba, bai yi wa hukumar zaben ta kasa dadi ba sam-sam.

A ranar Juma’a ne dai a lokacin wani taron manema labarai, Dr Briyai ya sanar da aniyarsa ta shiga wata jam’iyya domin tsayawa takarar gwamnan jihar Bayelsa, inda ya ce takarar tasa ta fara daga ranar 8 ga watan Agusta.

Hukumar INEC ta ce duk da cewa Dr Briyai ya bayyana aniyar tsayawa takarar ne a ofishin hukumar da ke birnin Calabar na jihar Cross Rivers, amma har yanzu ba su samu wata takarda daga wurinsa ba dangane da takarar tasa.

Wannan al’amari dai bai yi wa hukumar INEC dadi ba kamar yadda ta ce a wata sanarwa da ta fitar” Hukumar INEC ba ta ji dadin aniyar shugaban hukumar zaben jihar Cross Rivers ba ta shiga siyasa. Mun san cewa tsarin mulki ya hana ma’aikacin hukumar zabe shiga wata jam’iyya.”

Sanarwar wadda ke dauke da sa-hannun kwamishinan hukumar INEC mai kula da wayar da kan jama’a, ta kara da cewa “Yin amfani da farfajiyar ofishin hukumar da kayan hukumar ya saba doka sannan bai bi tanade-tanaden dokokin da’ar ma’aikata ba da ya kamata a ce duk jami’in hukumar INEC yana bi sau da kafa.”

Kwamishinan ya kuma ce jami’in hukumar tasu bai bi ka’idojin hukumar da ta gindaya na barin aiki ba.

Tuni dai hukumar INEC ta kori wannan jami’in nata dan takarar gwamna ba tare da bata lokaci ba, inda ta umarci sakataren gudanarwar hukumar da ya karbi ragamar aiki a jihar.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.