Soyayyar Gaske:- Tun Ina Yaro Nake Son Buga Wasa A Arsenal — David Luiz

44

- Advertisement -

Sabon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Dabid Luiz, ya bayyana cewa lokacin zamansa ne ya kare a Chelsea saboda haka ya yanke shawarar barin kungiyar zuwa kungiyar da tun yana matashin dan wasa yake burin bugawa wasa.

Kungiyar Arsenal ta kammala sayen dan wasan baya na Brazil Dabid Luiz daga Chelsea a kan kudi fan miliyan 8, a kwantiragin shekara biyu kuma Luiz, mai shekara 32, wanda kwantiraginsa zai kare a shekarar 2021, da Chelsea bai yi atisayi da tawagar manyan ‘yan kwallon kungiyar Chelsea ba a ranar Laraba.

Sai dai dan wasan mai shekara 32 ya halarci atisayen a Cobham, wato filin daukar horon kungiyar ta chelsea kuma bai bijire wa wani umarni ba – amma dai ba a yi komai da shi ba kamar yadda aka saba.

Bayan da Chelsea ta sayo dan wasan daga Benfica a watan Janairu na 2011, a kan fam miliyan 21, Luiz ya tafi PSG a watan Yuni na 2014 inda kungiyar ta Faransa ta saye shi a lokacin a kan fan miliyan 40, kafin kuma daga baya ya sake komawa Chelsea a Agustan shekara ta 2016 a kan fan miliyan 34.

Gaba daya ya yi shekara shida da rabi a Chelsea, inda ya dauki kofin gasar firimiya, da na FA biyu, da na Zakarun Turai na Champions da kuma na Europa guda biyu kuma ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan wasan baya na kungiyar.

A watan Mayu ya kulla wata yarjejeniya ta shekara biyu da Chelsea, kuma a yanzu ya bar kungiyar mako biyar bayan Frank Lampard ya koma kungiyar a matsayin kociya bayan Mauricio Sarri ya koma Juventus.

An haramta wa Chelsean sayen sababbin ‘yan wasa har zuwa watan Janairu na shekara ta 2020, sakamakon binciken da aka yi kan sayen ‘yan wasa na waje da suka yi ‘yan kasa da shekara 18 ba bisa ka’ida ba.

Yanzu ‘yan wasan baya da Chelsea take da su bayan tafiyar Luiz da kuma Gary Cahill wanda ya koma Crystal Palace a karshen kakar da ta wuce, sun hada da Antonio Rudiger, na Jamus, da Kurt Zouma, wanda a kakar da ta wuce yana zaman aro a Eberton,da kuma Andreas Christensen dan Denmark.

Arsenal za ta fara kakar Firimiya ta bana a gidan kungiyar kwallon kafa ta Newcastle, wadda itama ta adwo da tsohon dan wasanta, Andy Carrol daga Westham a ranar Lahadi, yayin da Chelsea za ta ziyarci Manchester United.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.