Tir kashi:- Real Madrid Ta Hakura Da Sayan Pogba

43

- Advertisement -

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta hakura da sayan dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba, bayan da aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a ranar Alhamis din data gabata a kasar Ingila.

Dan wasan dan shekara 26 a duniya dai ya kasance daya daga cikin ‘yan wasan da Real Madrid ta nema a wanann kakar bayan da kociyan kungiyar, Zinadine Zidane ya bayyana cewa yana bukatar dan wasan a cikin tawagarsa.

Sai dai shima dan wasan ya bayyana wa Manchester United cewa yanason barin kungiyar domin buga wasa a karkashin kociyan Real Madrid, wanda dan asalin kasar Faransa ne kuma wakilin dan wasan ya nuna a fili cewa yana bukatar barin kungiyar.

Manchester United dai ta yiwa dan wasan farashin fam miliyan 180 ga duk kungiyar da takeson daukar Pogba hakan yasa Real Madrid take ganin bazata iya bayar da kudin ba domin daukar Pogba wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018.

Sai dai za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ranar biyu ga watan Satumba ba kamar yadda aka rufe a kasar Ingila ba amma duk da haka Real Madrid tana ganin ba za ta iya jan hankalin Manchester United ta sayar mata da Pogba ba.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa Zidane ya zargi shugaban gudanarwar kungiyar, Florentino Perez, da rashin mayar da hankali wajen cinikin dan wasan sai dai watakila kungiyar zata iya komawa domin sayan dan wasan a kakar wasa mai zuwa.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.