Atiku Ya Kudiri Aniyar Amincewa Da Hukuncin Kotu

20

- Advertisement -

Tsohon Mataimakin shugaban Nijeriya Alh Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ya amince da hukuncin kotu.

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter cikin wani dogon rubutu da ya rubuta a shafin nasa. Inda ya bayyana cewa zai mika komai wurin Allah, domin shine mai yi.

Mataimakin shugaban kasar ya amince da hukuncin ne domin yiwa kotu biyayya, tare da yunkurin ciyarda Nijeriya gaba.

Akwai dai jita-jita da ake yadawar cewa tsohon mataimakin shugaban kasa bai taba rashin nasara a kotu ba sai wannan karo.

Sai dai kotu ta baiwa shugaba Buhari nasara tare da amincewa dashi a matsayin wanda ya lashe zabe a shekarar 2019.

Wasu na ganin cewa akwai yuyuwar idan Alh Atiku ya fito takara a zabe mai zuwa yayi nasara saboda duk Nijeriya yanzu babu dan siyasar da yake shugaban kasa wanda ya kai Alh Atiku karfi.

Musamman a bangaren siyasa dakuma yawan kudaden aiwatarda takara.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.