Dalilin da yasa muka kulle iyakokin Najeriya, Shugaba Buhari

34

- Advertisement -

A yau, Juma’ane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi bakuncin kingiyar ‘yan kasuwa da masana’antu na Najeriya da wasu kasashen Afrika a fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja.

A jawabinshi wajan ganawar tasu, Shugaba Buhari ya bayyana dalilin Najeriya na rufe iyakokinta na kan tudu, inda ya bayyana cewa an yi hakanne dan magance matsalar shigo da kaya marasa inganci da kuma wanda suka saba ka’ida yanda aka mayar da Najeriya kamar Bola.

Shugaban ya bayyana cewa abin takaicine yanda wasu ‘yan kasuwa sun saka riba a gaba maimakon kishin kasa inda suke taimakawa kamfanonin kasashen waje suna ci gaba amma na Najeriya da sauran kasashen Afrika na kara durkushewa. Yace ta iyakokinne ake shigo da miyagun kwayoyi da magungunan da basu da inganci da suke yiwa jama’a illa sannan kuma kayan wuta ma ana shigo da marasa inganci da a karshe ke jawo gobara da rasa rayuka. Yace yawancin wadannan kayayyaki ana shigowa dasune ta iyakar kasa.

Ya kara da cewa a dan lokacin da aka rufe iyakokin kasarnan har an fara samun saukin kayayyaki marasa inganci a kasuwanni, dan haka za’a ci gaba da rufe iyakokin na dan wani lokaci kamin samo hanyar da za’a magance matsalar.

Shugaban yace matakin an daukeshine dan inganta masana’antu da rayuwar ‘yan Najeriya dama yankin Afrika ta yamma da nahiyar baki daya, yace Najeriya kasar Kasuwancice kuma a shirye yake yayi aiki da ‘yan kasuwa dan ci gaban kasar amma ba za’a bari abubuwa su rika tafiya sakaka ba.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.