Fifa Ta Bukaci Kasar Iran Ta Fara Barin Mata Na Shiga Filin Wasa

13

- Advertisement -

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino ya ce ya kamata kasar Iran ta bai wa mata damar halartar filayen wasanni domin doka ta ba su dama a matsayinsu na mutane masu ‘yancin kansu.

Tun daga lokacin da aka kafa gwamnatin juyin juya hali a shekarar 1979 kasar ta Iran ta hana mata halartar filayen wasanni a lokacin da maza ke wasa sai dai Infantino ya ce yana fatan kasar za ta samar da wani sauyi kan wannan al’amari.

A watan gobe ne kasar Iran din za ta karbi bakuncin wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya da za ta kara da Cambodia kuma a wasanni ake ganin yakamata hukumomin kasar su fara girmama kiran da Fifa tayi.

“Burinmu a bayyana yake saboda ya kamata Iran ta bawa mata dama su rika halartar kallon wasanni a filin wasanni saboda hakan zai sanya farin ciki a zukatansu kuma zasu samu karfin guiwar shiga harkokin wasanni,” in ji Infantino

Ya ci gaba da cewa “Yanzu lokaci ne da ya kamata a bullo da sauye-sauye kuma FIFA tana jiran sakamako mai faranta rai, kuma muna son ya fara aiki ne a wasan da Iran din za ta karbi bakuncinsa a watan Oktoba.”

A farkon watan Satumbar shekara ta 2019 ne wata mace mai suna Sahar Khodayari ta rasu bayan da ta cinnawa kanta wuta, sakamakon hana ta shiga gidan kallo da aka yi a kasar ta Iran din wanda wannan lamari ne yaja hankalin Fifa.

Matashiyar wadda aka yi wa lakabi da “Blue Girl” an cafke ta a watan Maris, lokacin da take kokarin shiga wani gidan kallo inda jami’an tsaro suka cafketa kuma suka bawa hukuma ita domin hukunci.

A gasar cin kofin nahiyar Asiya da aka fafata a watan Nuwambar bara, an bar mata magoya bayan kwallon kafa halartar gidajen kallo amma a watan Yuni an hana mata halartar gidajen kallo a wasan sada zumuncin da Iran din ta yi da kasar Syria a filin wasa na Azadi da ke babban birnin kasar Tehran.

A ranar 10 ga watan Oktoba ne Iran din za ta kara da kasar Cambodia a wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya kuma kamar yadda Fifa ta bukata, ana ganin kasar ta Iran zata girmama kiran na hukumar kwallon kafar duniya.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.