Harin bindiga ya kashe mutum 2 a babban birnin kasar Amurka

14

- Advertisement -

Mutum 1 ya rasa ransa, wasu 5 sun samu raunuka sakamakon hari da bindiga da aka kai a Washington Babban Birnin Kasar Amurka.

Labaran da jaridun Amurka suka fitar sun rawaito jami’an ‘yan sanda na cewa an kai harin da bindiga a yankin Columbia Hieghts dake da nisan kilomita 3 daga Fadar White House inda mutum daya ya mutu, wasu 5 kuma suka samu raunuka.

Biyu daga cikin mutanen da suka jikkata na cikin mawuyacin hali a asibitin da aka kai su.

Jami’an ‘yan sanda sun ce har yanzu ba a kama wanda ya kai harin ba amma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Kasa da awa daya bayan faruwar harin farko an kuma sake samun rahoton wani harbin inda aka harbi mutum 3, daya daga cikinsu ya mutu.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.