Ina Son Wuce Messi A Wajen Lashe Gwarzon Duniya — Ronaldo

45

- Advertisement -

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo ya ce yana fatan sake lashe kyautar Ballon d’Or akalla sau biyu ko uku kafin ritayarsa daga fagen kwallon kafa kuma yana fatan wannan mafarkin nasa zai zama gaskiya.

Ronaldo, wanda ya lashe kyautar ta Ballon d’Or har sau 5 dai dai da Lionel Messi na Argentina da ke buga wasa a Barcelona, a wata tattaunawarsa da manema labarai ya ce yana fatan wuce takwaran nasa yawan kyautukan Ballon d’Or.

Ronaldo dan asalin kasar Portugal mai shekaru 34 ya ce duk da kasancewarsa a jerin ‘yan wasan kwallon kafa da suka kafa gagarumin tarihi a fagen, yana fatan sake kafa wani tarihin kafin barinsa filin wasa.

“Ina da karfi da kuma kwarin guiwar cewa zan iya bawa duniya mamaki ta hanyar lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya anan gaba saboda burina a koda yaushe shine cigaba da kafa tarihi a duniya’

Bayan nasarar Luka Modric ta lashe ballon d’Or a bara, shekaru 10 da suka gabata ‘yan wasan biyu su ke lashe kyautar, yayinda ko a bana ma dai sunayen Cristiano Ronaldon da Lionnel Messi na cikin wadanda ake saran su iya lashe kyautar ta Ballon d’Or tare da Birgil ban Dijk na Liberpol dan kasar Holland.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.