Mourinho Yana Jiran Real Madrid Ta Kori Zidane — Rahoto

44

- Advertisement -

Manchester United’s Portuguese manager Jose Mourinho gestures towards the public at the end of the UEFA Champions League group H football match Juventus vs Manchester United at the Allianz stadium in Turin on November 7, 2018. (Photo by Marco BERTORELLO / AFP)

Bakin mai koyarwa Zinedine Zidane har kunne a wata shida da suka wuce yana cewa ya ji dadi sosai da ya dawo gida a matsayin kocin Real Madrid a karo na biyu sai dai murnar ta koma ciki biyo bayan yadda kungiyar ta fara buga wasa a kakar bana, abin da ya kara jawo wa dan kasar Faransar matsin lamba a Real Madrid.

Bayan Real Balladolid da Billarreal sun rike su canjaras a filin wasa na Santiago Bernabeu, sai ga kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German

ma ta casa su da ci 0-3 a gasar kofin zakarun turai na Champions League a daren Larabar data gabata.

Mece ce makomar shahararren kociyan wanda ya jagoranci Real Madrid zuwa ga nasarorin lashe kofin Champions League har uku a jere kuma wane ne zai maye gurbinsa idan ya bar Real Madrid nan gaba?

“Da zarar ka ji irin wannan sakamakon dole ne ka fara duba yanayin da kungiya take ciki kamar yadda kwararren dan jarida mai sharhin wasannin LaLiga Guillem Balague ya shaida wa manema labarai.

Ya ci gaba da cewa “Ku saurari abin da ‘yan jaridar da ke kusa da Florentino Perez (shugaban Real Madrid) suke cewa, idan suka fara sukar Zidane to ku tabbatar kofa ta bude kenan kuma komai zia iya faruwa.”

Makin cin wasa na Zidane a Real Madrid yana kasa da kashi 50% tun bayan dawowarsa a karo na biyu haka zalika, wasa bakwai kacal ta ci cikin 16 a LaLiga da Champions League a karkashin Zidane ta ci biyar, ta yi canjaras hudu.

Sai dai Julien Laurens, shi ma mai sharhi kan wasannin, bai yarda Zidane zai bar Real Madrid ba, inda ya ce ya san matsalolin kungiyar da ma yadda zai gyara al’amura kuma ya san cewa a karshe abubuwa za su warware.

Ya kara da cewa ba mutumin da zai karaya ba ne saboda ya san matsalolin da ya kamata ya gyara kuma wannan tsakiyar ta Real Madrid ba ta yi kama da ta babbar kungiya ba saboda haka

wajibi ne ya gano bakin zaren.

Real Madrid ba ta yin wata-wata duk sanda ta amince cewa tana bukatar canji a dakin shiryawar ‘yan wasanta sai dai ta yi jira har zuwa karshen watan Oktoban bara kafin ta sallami Julen Lopetegui a kakar da ta gabata wata hudu da rabi ya yi.

Shi kuwa Santiago Solari, wanda ya gaji Lopetegui, an kore shi ne kasa da wata biyar bayan fara horar da kungiyar abin da ya share fagen dawowar Zidane sai dai idan ya yi sa’a kamar yadda ya faro aikinsa babu mamaki ya kai karshen kakar bana.

Sai dai salon kwallon kungiyar a yanzu ba shi da kyau ko da kuwa kaftin din kungiyar Sergio Ramos da Marcello da Modric sun dawo ba lallai ne su ishe shi ba ya kai har Disamba a gefe guda kuma, dan jarida Kristof Terreur na kasar Belgium sukar kociyan ya yi.

Dan jaridar yace “me Zidane ya kara wa kungiyar? Mene ne salon wasansa? Har yanzu babu tabbacin yadda aka yi Real Madrid ta lashe Champions League har sau uku a jere saboda haka akwai alamar tambaya” a cewar Terreur.

An yi ta alakanta Mourinho da aikin horar da Real Madrid idan har aka kori Zidane kuma kamar yadda aka sani a shekarar 2013 ne Mourinho ya bar kungiyar bayan zaman shekara uku yanzu haka ba shi da aiki bayan Manchester United ta sallame shi a Disambar shekara ta 2018.

“Ina zaton Jose Mourinho zai karbi aikin nan da Disamba saboda Real Madrid na bukatar mutum kamar Mourinho wanda ke iya buga wasan tsare baya sannan kuma ‘yan wasan ma suna bukatar horo daga tsayayyen koci kamarsa.” cewar Terreur.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.