Muna Buga Wasa Kamar Yara Kana na, Cewar Harry Kane

25

- Advertisement -

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Harry Kane ya ce kungiyarsa ta Tottenham ba ta koyi darasi ba game da kwallo biyu da suka bari aka farke a wasansu da Olympiakos a gasar kofin zakarun turai na Champions League a daren Larabar data gabata.

Duk da kwallo biyu da suka zura a raga ta hannun finaretin da Kane din ya ci da kuma kwallon da Lucas Moura ya dada a raga, wasan ya tashi 2-2 wanda hakan ya bawa kociyan kungiyar haushi sosai.

“Ka duba yadda ran kociyan mu ya baci saboda yana tare da mu tsawon shekara biyar amma har yanzu muna yin kuskuren da muka saba yi saboda haka akwai bukatar muyi karatun ta nutsu akan abinda muke aikatawa.” In ji dan wasan gaban.

Kane ya ci gaba da cewa “Mu fa yanzu ba yara ba ne, ba za a ce ba mu da kwarewa ba saboda

mun buga manyan wasanni a matakin kasa da na kungiya saboda akwai bukatar mu dinga tunani sama dana kana nan ‘yan kwallo.”

Kazalika Tottenham ta barar da damar nasararta a wasan hamayyar birnin Landan a filin wasa na Emirate ranar 1 ga watan Satumba, inda suka ci 2 kuma aka farke wasa ya tashi 2-2 wanda hakan shima ya batawa kociyan kungiyar rai sosai.

A karshe Kane ya ce lallai ya kamata su bi hanyoyin gyarawa domin su kyuatata harkar kwallonsu idan kuma ba su dauki mataki ba babu inda za su je kuma ba za su iya cika burinsu ba wanda suke niyyar ganin ya tabbata.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.